
Shugabannin Matasa Na Arewa Sun Bukaci Gaskiya Da Bayyananniyar Manufa a Sabon Taron Gwamnatin Tarayya da Yankin Arewa
Shugabannin Matasa Na Arewa Sun Bukaci Gaskiya Da Bayyananniyar Manufa a Sabon Taron Gwamnatin Tarayya da Yankin Arewa
Ƙungiyar Shugabannin Matasa ta Arewa (Northern Nigeria Youth Leaders Forum - NNYLF) ta bayyana damuwarta kan shirin Gwamnatin Tarayya na gudanar da wani taro da ake shirin yi a Arewa, inda suka buƙaci gaskiya, haɗin kai, da girmama ikon yankin Arewa wajen gudanar da duk wani tattaunawar kasa.
A wata taron manema labarai da aka gudanar a NUT-End Well Hotel da ke Magadishu Layout, Kaduna, kungiyar ta nuna rashin jin daɗinta game da haɗin gwiwar da ake yi da Gidauniyar Tunanin Sir Ahmadu Bello domin shirya wani taron da ake cewa zai nuna abin da gwamnatin tarayya ta cimma a yankin Arewa. Kungiyar ta bayyana taron a matsayin wanda ba shi da gaskiya, babu bayyananniya, kuma yana nuna wariyar wasu daga cikin 'yan Arewa da suka dace su kasance cikin tsarin.
Da yake jawabi a madadin kungiyar, Muhammad Isah Imam, Sakataren Harkokin Yada Labarai da Jama'a, ya soki Gwamnatin Tarayya bisa “sauyin kwatsam na nuna kulawa” bayan kusan shekaru biyu tun bayan taron Kaduna na Oktoba 2022. Taron da aka gudanar a wancan lokaci ya haɗa dukkan masu neman takarar shugaban ƙasa tare da manyan ƙungiyoyin Arewa, kuma an yaba da shi a matsayin alamar dimokuraɗiyya ta gaskiya.
“Me ya sa yanzu?” in ji Imam. Ya ci gaba da tambaya, “Shin wannan sabon taro wata hanya ce ta magance matsalolin da suka jima suna addabar yankin Arewa ko kuwa wata dabara ce ta siyasa domin lulluɓe matsaloli da nufin kwantar da hankali?”
Kungiyar ta ambato matsalolin da suka daɗe suna addabar Arewa kamar rashin ci gaba, rashin tsaro, da watsi da yankin duk da yawan jama’arsa da albarkatun da yake da su. Sun jaddada cewa duk wani sabon shiri dole ne ya kasance bisa gaskiya, adalci, da kuma cikakken haɗin kai na dukkan masu ruwa da tsaki daga yankin—musamman matasa, mata, kungiyoyin farar hula, shugabannin addinai da na gargajiya.
Daga cikin tambayoyin da suka taso sun haɗa da:
Rashin bayani a fili game da manufa da tsarin taron;
Ware kungiyoyin da suka shirya taron Kaduna na 2022;
Tsoron karfa-karfa daga Gwamnatin Tarayya a wani abu da ya kamata Arewa ce ke jagoranta;
Tambayoyi kan dalilin zaɓar Gidauniyar Sir Ahmadu Bello kawai a matsayin abokin haɗin gwiwa, ba tare da sauran masu ruwa da tsaki ba.
Kungiyar ta kuma bayyana damuwarta kan shiru da rashin tsayawa tsayin daka daga wasu dattawan Arewa da suka taka rawa a gabanin taron 2022, tana tambaya ko sun yarda da tsarin ko kuwa an basu gefe.
Don haka kungiyar ta gabatar da buƙatu kamar haka:
1. Bayyana a fili manufa, ajanda, da sakamakon da ake sa ran samu daga taron da ake shirin gudanarwa;
2. Cikakken haɗa duk masu ruwa da tsaki daga Arewa cikin tsarin;
3. Mayar da ikon taron zuwa hannun 'yan Arewa da kungiyoyinsu, ba wai gwamnati ta ci gaba da jan ragamar ba;
4. Tabbatar da irin wannan taro a kowanne yanki na ƙasar domin adalci da daidaito;
5. Bayani daga shugabannin da suka jagoranci taron 2022 game da matsayin su a wannan sabon ci gaban.
Ƙungiyar Shugabannin Matasa ta Arewa ta tabbatar da cewa tana da niyyar ci gaba da tattaunawa ta kwarai da gaske, amma ta ƙi amincewa da duk wata alamar nunawa ko cin mutunci ga yankin Arewa cikin tsarin gwamnatin tarayya.
“Ba mu 'yan kallo ba ne a makomar mu,” in ji Imam. “Arewa na buƙatar taro na gaskiya, ba shiri irin na nunin siyasa ba. Matasanmu suna sane da duk wani abu da ke faruwa, kuma mun shirya kare muradun mu ta hanya mai tsafta da lumana.”
Jawabin ya ƙare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba al’amura, ta rungumi gaskiya da adalci, tare da gudanar da duk wani shiri da Arewa cikin mutunci da gaskiya domin guje wa ƙarin rashin yarda da rashin haɗin kai.